27 Faburairu 2021 - 09:31
Zababben Shugaban Kasar Nijar, Muhammadu Bazoum Ya Daga Hannun Jinjina Ga Abokin Karawarsa Muhammadu Usmana

A wani jawabi da zababben shugaban kasar ta Nijar, Muhammadu Bazoum ya yi bayan sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben, ya yi godiya ga Allah madaukakin sarki wanda ya dora masa wannan nauyi na shugabancin kasar, sannan kuma ya yi jinjina ga al’ummar kasar ta Nijar.

ABNA24 : Muhammadu Bazoum ya kuma ce; Mun kammala zaben wanda ya dauki lokaci ana yi a ranar Lahadi 21 ga watan Febrairu. Sakamakon zaben na wucin gadi da hukumar zabe ta fitar ya tabbatar da cewa ni ne na lashe zaben da kaso 55.75, don haka ni ne zababben shugaban kasa.”

Wani sashe na jawabin zababben shugaban kasar ya kunshi alkawalin yin kokawa domin kawar da rashin tsaro da ake fama da shi a kasar.

A wani labarin daban daga kasar ta Nijar,Zanga-zanga ta barke bayan sanarda Muhammadu Bazoum a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasa.

Magoya bayan Muhammad Usmana sun datse hanyoyin a babban birnin kasar Niamy, tare da kona tayoyi domin kin amincewarsu da sanarwar hukumar zabe na cewa; Muhammadu Bazoum ne ya lashe zaben shugaban kasar zagaye na biyu.

342/